エピソード

  • Matakan Da Wasu Al’ummomi Suke Dauka Don Guje Wa Ambaliyar Ruwa
    2024/09/19

    Send us a text

    Wasu al’ummomi a Najeriya sun fara ɗaukar matakan kauce wa asarar da ambaliyar ruwa ka iya haifar musu idan aka buɗe Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.

    A kwanan nan ne dai Hukumar da ke Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya ta ce yankunan da ke gaɓar Kogin Binuwai a jihohi 11 na fuskantar barazanar ambaliyar.
    Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan wadannan matakai da ma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.

    続きを読む 一部表示
    22 分
  • ‘Mun Yi Zaton Samun Sauki Da Zuwan Matatar Dangote’
    2024/09/17

    Send us a text

    ‘Yan Najeriya sun yu ta sa ran zuwan matatar Dangote zai samar da saukin wahalhalun man fetur.

    Sai dai tun ba a je ko ina ba ana ta samun musayar kalamai tsakanin kamfanin NNPCL da Dangote kan batun.

    Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda farshin man fetur ke ci gaba da karuwa duk da zuwan matatar Dangote

    続きを読む 一部表示
    23 分
  • “Akwai Yiwuwar Maimaita Ambaliyar Borno A Wasu Jihohin”
    2024/09/16

    Send us a text

    Rahotanni sun ce al’ummomin wasu yankuna a wasu jihohin Najeriya suna zaman ɗar-ɗar bayan da ruwa ya fara mamaye gonaki da gidajensu.

    Tun bayan mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, hukumomi a Najeriya suke kara ankarar da al'ummomin wasu jihohin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar.

    Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda za a dauki matakan kan-da-garki kan yiwuwar ambaliyar.

    続きを読む 一部表示
    14 分
  • Yadda Mazauna Maiduguri Za Su Kubuta Daga Illolin Ambaliya
    2024/09/13

    Send us a text

    Bayan mummunar ambaliyar ruwar da ta mamaye kusan kashi 70 cikin 100 na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, masana na bayyana fargaba game da yiwuwar barkewar cututtuka da kuma ta'azzarar manyan larurori ga masu dauke da su.

    Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan yadda al'ummar birnin na Maiduguri za su kare kansu kuma su tsira da lafiyarsu.

    続きを読む 一部表示
    25 分
  • Shin Dole Ne Sai An Dauki Tsauraran Matakan Saita Najeriya?
    2024/09/12

    Send us a text

    Duk da kokawa da Yan Najeriya ke ci gaba da yi kan irin manufofin gwamnati da suka ce suna Kara jefa su cikin kangin rayuwa.

    Amma, a ko da yaushe Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Yana kara nanata cewa, tilas ne a dauki tsauraran Matakai na saita tattalin arzikin kasar, idan har ana bukatar Jin dadi a nan gaba.

    Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne, kan ko tilas ne sai an dauki tsauraran Matakan, kafin saita tattalin arzikin Najeriya?

    続きを読む 一部表示
    24 分
  • Dabarun Magance Matsalolin Najeriya
    2024/09/10

    Send us a text

    Daga cikin manyan hakkokin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dorawa shugabanni, shine kirkirar dabarun samarwa Yan kasa saukin tsadar Rayuwa da tabbatar da kasancewar su cikin walwala.

    Sai dai, a baya-bayan nan, Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin gamsuwa irin dabarun da shugabanninin ke amfani dasu wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna ne, kan irin dabarun da suka kamata shugabanninin Najeriya suyi amfani dasu, wajen magance matsalolin da ake ciki.

    続きを読む 一部表示
    27 分
  • 'Karin Farashin Mai Ya Fara Tilasta 'Yan Najeriya Ajiye Aiki'
    2024/09/09

    Send us a text

    Karin farashin man fetur da NNPCL ya yi a baya-bayan nan, na kara jefa 'yan Najeriya cikin kunci da rashin tabbas a rayuwar yau da Kullum.

    Tsadar kayayyaki musamman na abinci da sufuri, ya fara tilasatawa wasu Ma'aikata ajiye aiyyukan su

    Shirin Najeriya a Yau ya zai yi dubi kan illar yanayin ga wadanda abin ya shafa, da ma tattalin arzikin kasa.

    続きを読む 一部表示
    24 分
  • Mece Ce Illar Zub-Da Kimar Najeriya A Kasashen Ketare?
    2024/09/06

    Send us a text

    Sau da dama, ana yawan batun yadda 'yan Najeriya ke bata wa kasar suna sakamakon ayyukan assha da suke aikata wa a kasashen ketare

    Wasu na alakanta wannan lamari da yadda ake ganin 'yan wasu kasar na yiwa 'yan Najeriyar gani-gani a kasashen nasu.

    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan ne, kan wannan batu.

    続きを読む 一部表示
    25 分