エピソード

  • Abin Da Ya Hana Dalibai Da Dama Komawa Makaranta
    2024/09/18

    Sama da mako guda ke nan bayan komawa makarantu domin fara sabon zangon karatu a kusan dukkanin sassan Najeriya.

    Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, ana samun karancin komawar dalibai makaranta a wasu sassan kasar.

    Shirin Daga Laraba na wananan makon zai yi duba ne a kan dalilan faruwar hakan.

    続きを読む 一部表示
    25 分
  • Ribar Da ’Yan Najeriya Za Su Samu Daga Hulda Da China
    2024/09/11

    Dangantaka ko alaka a tsakanin Najeriya da China tana ƙara yaukaka, musamman a baya-bayan nan.

    Ko a kwanan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar ta China domin halartar taron kyautata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka.

    Shirin Daga Laraba na wananan mako zai tattauna a kan ko mecece ribar ’yan Najeriya a irin wannan dangantakar?

    続きを読む 一部表示
    29 分
  • Me Ya Kamata A Yi Lokacin Komawar Yara Makaranta?
    2024/09/04

    A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu.

    Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a Najeriya?

    Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan wannan batu na komawa makanta bayan hutun dogon zango.

    続きを読む 一部表示
    22 分
  • Muhimmancin Al'adar Ciyayya.
    2024/08/28

    Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum.

    Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare.

    Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan muhimmancin wannan Al'ada, musamman la'akari da irin halin da ake ciki yanzu a Najeriya.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • Me Ya Kamata A Yi Wa Mutanen Da Rikicin Ta’addanci Ya Rutsa Da Su?
    2024/08/21

    Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su.

    A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda
    2024/08/14

    A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna.

    A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya.

    To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi bayani kan abin da ke faruwa a duk lokacin da bankuna suka yi maja a waje da juna.

    続きを読む 一部表示
    23 分
  • Yadda Za Ku Gane Shafukan Tallafin Gwamnati Na Bogi
    2024/08/07

    Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma.

    Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan intanet na tallafin gwamnati na bogi da na gaske.

    続きを読む 一部表示
    24 分
  • Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Idan Tana Son Hana Zanga-Zanga
    2024/07/31

    Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka.

    Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma.

    Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.

    続きを読む 一部表示
    28 分